Gwamnatin Tarayya ta gabatar da buƙatar ƙarin Naira tiriliyan ₦6.2 akan kasafin kuɗi, wajen biyan mafi karancin albashi.
Ministan Kasafin Kudi da Tsare-Tsare na Kasa Atiku Bagudu ne, ya bayar da wannan tabbacin lokacin da yake jawabi ga kwamitin kasafin kudi na majalisar wakilai a Abuja.
Ya ce za a kashe kudaden ne wajen inganta tattalin arzikin kasar ta hanyar aiwatar da ayyukan more rayuwa, inda ya ce Naira tiriliyan uku ne za a biya sabon mafi karancin albashin ma’aikata, wanda Shugaban kasa Bola Tinubu ya ce nan ba da dadewa ba za a aika da kudirin ga ‘yan Majalisa.
Wannan kuma ya hada da kashe Naira tiriliyan 3 na sabon tsarin mafi karancin albashi da Shugaban kasar ya mikawa majalissa.
Bichi ya lura da cewa akwai bukatar a yi wa ‘yan Najeriya cikakken bayani game da kasafin kudin da ake shirin yi na Naira Tiriliyan 6.2.