Gwamnatin tarayya ta fara tantance fursunoni a cibiyoyin gyaran hali 256 na kasar nan da nufin rage cunkoso a gidajen gyaran hali

Gwamnatin tarayya ta ce ta fara tantance fursunonin a cibiyoyin gyaran hali 256 na kasar nan, da nufin rage cunkoso a gidajen gyaran halin.

Ministan harkokin cikin gida, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo ne ya bayyana hakan bayan kammala ziyayar gani da ido a wani aikin gidan gyaran hali mai daukar mutane 3,000 da ke gudana a Janguza jihar Kano da kuma gidan gyaran hali da ke Kuje, a Abuja.

A harabar Kuje, ministar ya samu kyautar litattafai uku da daya daga cikin fursunonin da ke tsare shekaru 12 da suka gabata ya rubuta.

Tunji-Ojo wanda ya nuna farin cikinsa, ya ce, wuraren ba gidan yari ba ne, amma cibiyoyin gyaran hali ne don gyara wadanda aka kama da laifi bisa doka.

Comments (0)
Add Comment