Gwamnatin tarayya ta dakatar da amincewa da sabbin ayyukan tituna a fadin kasar nan, kamar yadda ministan ayyuka David Umahi ya sanar a jiya Lahadi a garin Calabar. Wannan shawarar ta biyo bayan umarnin shugaban ƙasa Bola Tinubu, inda gwamnatin za ta mayar da hankali wajen kammala ayyukan a cikin kasafin kuɗin shekarar 2025 mai zuwa. Ministan ya kuma soki yadda ake tafiyar da kwangilar gina hanyar gwamnatin tarayya ta Odukpani-Itu, inda ya gargadi ƴan kwangilar da su koma wurin aikin ko kuma su fuskanci soke kwangilar. Ya jaddada fa’idar tattalin arzikin hanyar Legas zuwa Calabar, wadda za ta taimaka wajen haɓɓaka kasuwanci da tattalin arziki. Gwamnan jihar Cross River, Bassey Otu, ya yi alƙawarin bayar da cikakken goyon baya ga aikin, inda ya bayyana muhimmancinsa ga ci gaban tattalin arziƙin yankin.