Gwamnatin tarayya na sa ran karɓar rancen dala biliyan 2.2 daga bankin duniya

Gwamnatin tarayya na sa ran karɓar rancen dala biliyan 2.2 daga bankin duniya da kuma wani tallafin daga bankin raya ƙasashen Afirka, AfDB.

Ministan kuɗi, Wale Edun ne ya bayyana haka yayin wani taron manema labarai na haɗin gwiwa a ƙarshen tarukan bankin duniya da IMF a birnin Washington DC da ke Amurka.

Da yake magana kan hanyoyin samun kuɗaɗe don tallafa wa tattalin arzikin Najeriya, Edun ya lissafa kuɗaɗen da ƴan Najeriya mazauna ƙetare ke tura wa ƙasar da hannun jari da cibiyoyin bankin duniya da sauran ƙungiyoyin samar da ci gaba na ƙasashen duniya.

Ya ƙara da cewa Najeriya za ta kuma amfana daga tallafin kasafin kuɗi da yake da kuɗin ruwa ƙalilan daga bankin raya ƙasashen Afirka inda ya ce ana tattaunawa da ƴan ƙasashen waje masu zuba hannun jari. Edun ya bayyana cewa kuɗin da ake samu daga man fetur ne babbar hanyar samun kuɗin shiga ga Najeriya sannan ƙudirin shugaban Najeriya Bola Tinubu na ƙara samar da ɗanyen mai daga ganga miliyan 1.6 duk rana zuwa ganga miliyan biyu kowace rana.

Comments (0)
Add Comment