Gwamnatin Sojin Nijar ta saki wasu fursunonin siyasa aƙalla 50

Gwamnatin Sojin Nijar ta saki wasu fursunonin siyasa aƙalla 50 ciki har da tsaffin ministocin gwamnatin da aka hamɓarar a juyin mulkin watan Yulin 2023, afuwar da ke matsayin wani ɓangare na matsayar da aka cimma a taron ƙasa da ya gudana a cikin watan Fabarairu. 

Mutanen da aka saki ƙarƙashin umarnin shugaban mulkin Sojan na Nijar sun ƙunshi tsaffin ministoci, jami’in Diflomasiyya guda da kuma ɗan Jarida baya ga Sojojin da aka zarga da kitsa juyin mulkin 2010.

Sai dai har yanzu Sojojin na ci gaba da tsare hamɓararren shugaba Mohamed Bazoum duk kuwa da kiraye-kirayen ƙasashe na ganin an sake shi daga haramtacciyar tsarewar da ake masa.

Sanarwar da Sojin da aka karanta ta gidan talabijin ta ce an saki dukkanin mutanen ne bisa matsayar da aka cimma a taron na ƙasa.

Dukkanin mutanen an kame su ne jim kaɗan bayan juyin mulkin da Janar Abdourahamane Tiani tsohon shugaban jami’an tsaron fadar shugaban ƙasa ya jagoranta, ta yadda aka riƙa sauya musu gidajen yari daga wani zuwa wani.

Comments (0)
Add Comment