Gwamnatin mulkin sojin Jamhuriyar Nijar ta sanar da soke duk wata yarjejeniya tsakanin ƙasar da ƙungiyar bayar da agaji ta Red Cross
Hukumomin sun kuma rufe ofisoshin ƙungiyar a faɗin ƙasar da kuma korar duk ma’aikatan ƙungiyar da ba ƴan ƙasar ba.
Duk da dai ba a san dalilin yin hakan ba zuwa yanzu, an jima ana samun rashin jituwa tsakanin ɓangarorin biyu tun watan Nuwamban bara, lokacin da ‘hukumomin Nijar suka nuna damuwa kan yadda ake tafiyar da tallafin jin-ƙai da Tarayyar Turai take bai wa ƙungiyoyin masu zaman kansu, ciki har da Red Cross.’
Hukumomin sojin kasar sun furta cewa kungiyoyin ba su gudanar da ayyukansu a cikin hanyoyin da suka dace kamar yadda dokoki da yarjeniyoyi suka tanada ta hanyoyin hulda ta kasa da kasa.
Red Cross (Croix Rouge) ta kasance a kasar ta Jamhuriyar Nijar tun shekara ta 1990, inda kuma ta kara kaimi wajen gudanar da ayyukanta a cikin kasar daga shekara ta 2007.
A lokacin da kungiyar ƴan tawaye ta MNJ ta fara gudanar da ayyukan tayar da kayar baya a cikin kasar ta Jamhuriyar Nijar, kungiyar ta cigaba da taimaka wa alummar da suka tsere daga gidajensu ta hanyar samar masu da ruwan sha da sauran buƙatu.
A watan Nuwamba hukumomin sojin kasar sun dakatar da kungiyoyi biyu masu zaman kansu ba tare da sanar a hukumance ba hujojin da suka kawo ga hakan.
Kungiyoyin sun hada da ACTED Agency for Assistance for Cooperation and Development ko kuma Agence da la coperation pour l’assistance au Developpement da kuma APBE.
– BBC Hausa