Gwamnatin Najeriya zata dauki mataki kan duk wata kasa da ke da hannu wajen zanga-zanga a kasar

Gwamnatin Najeriya ta yi barazanar daukar matakin da ya dace kan duk wata kasa ko kuma wasu muradun kasashen ketare da ke da hannu wajen zanga-zanga a Najeriya.

Ministan Harkokin Waje, Ambasada Yusuf Tuggar, wanda ya yi wannan gargadin a lokacin da yake jawabi ga jami’an Diflomasiyya a Abuja ranar Laraba, ya ce Najeriya kasa ce mai cin gashin kanta, kuma ba za ta lamunta da duk wani katsalandan a cikin harkokinta na cikin gida da wasu kasashen waje ke ba masu zanga-zangar goyon baya ba.

Wannan matsayi na gwamnati ba zai rasa nasaba da rahoton da aka samu na masu zanga-zangar da ke daga tutar kasar Rasha tare da yin kira ga shugaba Vladimir Putin da ya kai dauki ga ‘yan Najeriya a cikin yunwa da kuncin rayuwa da ke addabar mafi yawan al’ummar kasar.

Kafofin yada labarai sun ruwaito cewa, kasar Rasha ta bakin ofishin jakadancinta da ke Abuja, ta nesanta kanta daga masu zanga-zangar da ke daga tutarta tare da musanta cewa tana da hannu wajen shirya zanga-zangar.

Zanga-zangar da ta fara a ranar 1 ga watan Agusta a fadin kasar nan da nan ta rikide zuwa tashe-tashen hankula, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane da sace-sace da kuma lalata dukiyoyi.

Comments (0)
Add Comment