Gwamnatin Najeriya ta cika sharuɗɗan taso ƙeyar Simon Ekpa daga Finland

Babban hafsan tsaro na Najeiya Janar Christopher Musa ya ce gwamnatin tarayya ta cika akasarin sharaɗin neman taso ƙeyar Simon Ekpa daga ƙasar Finland.

Jami’an tsaron Finland sun kama Ekpa, wanda ɗan gwagwarmayar kafa ƙasar Biafra ne a kudu maso gabashin Najeriya, a watan Nuwanban da ya gabata.

Daga baya wata kotu ta aika shi gidan yari saboda kama shi da laifin yaɗa manufofin ta’addanci a kafafen sada zumunta.

“Gwamnatin tarayya ta tura mafi yawan abubuwan da ake buƙata ga gwamnatin Finland,” in ji janar ɗin yayin da yake magana a shirin talabijin na Channels TV.

“Ba ni son faɗar abubuwa da yawa a kansa amma ina da tabbas za a yi abin da ya dace.”

– BBC Hausa

Comments (0)
Add Comment