Gwamnatin tarayya ta ayyana ranakun Laraba 25, da Alhamis 26, Disamba, 2024, da kuma Laraba 1 ga Janairu, 2025, a matsayin ranakun hutu domin bukukuwan Kirsimeti, Boxing da kuma sabuwar shekara.
Ministan harkokin cikin gida, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo, wanda ya bayyana hakan a madadin gwamnatin tarayya a safiyar jiya Litinin, ya mika sakon taya murna ga daukacin al’ummar kasar, inda ya bukace su da su yi amfani da lokacin bukukuwan wajen yin tunani a kan kimar soyayya, zaman lafiya, da hadin kai da wannan ranakun ke nunawa. Tunji-ojo, a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban sakataren ma’aikatar, Dakta Magdalene Ajani, ta kara jaddada muhimmancin wannan ranakun na bana a matsayin lokacin da za a samar da zaman lafiya da karfafa zumunci a tsakanin iyalai da al’umma. Ministan ya kuma taya kiristoci da daukacin ‘yan kasar mazauna gida da na kasashen waje murnar zagayowar wannan rana.