Gwamnatin Najeriya na duba yiwuwar hada gwiwa da bankin duniya domin bunkasa fannin hakar ma’adanai

Gwamnatin tarayya ta hannun ma’aikatar bunkasa ma’adanai tana duba yuwar ta hada gwiwa da bankin duniya domin bunkasa fannin hakar ma’adanai a kasar nan.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai taimaka wa ministan ma’aikatar ma’adanai  kan harkokin yada labarai, Segun Tomori kuma aka rabawa manema labarai a yau talata.

Da yake jawabi yayin wata ziyarar ban girma da ya kai wa Ministan ma’adanai na kasa, Dele Alake, jiya, daraktan bankin duniya a kasa, ya bayyana jin dadinsa bisa wannan hadin gwiwa da gwamnatin tarayyar zata yi da bankin. Ya nanata shirin bankin na yin hadin gwiwa da ma’aikatar, wajen samar da kudade na musamman da kuma tabbatar aiwatar da ayyuka yadda ya kamata a kasar nan.

Comments (0)
Add Comment