Gwamnatin kasar Chadi a jiya ta ce ta dakile wani yunkurin tada zaune tsaye da jami’an sojoji da wani fitaccen mai fafutukar kare hakkin bil’adama suka yi.
A cewar sanarwar da gwamnatin kasar ta fitar, wasu gungun jami’am sojoji 11 ne karkashin jagorancin Baradine Berdei Targuio, shugaban kungiyar kare hakkin bil’adama ta kasar Chadi, suka yi wannan yunkurin.
Sanarwar ta kara da cewa jami’an tsaro sun fara kama wadanda suka aikata wannan aika-aika ne daga ranar 8 ga watan Disamba.
A watan Fabrairun 2021 ne aka yanke wa Berdei Targuio hukuncin zaman gidan yari na tsawon shekaru uku, bisa zarginsa da take tsarin mulkin kasar, saboda ya rubuta cewa shugaban kasar Chadi na lokacin, Janar Idriss Deby Itno, na fama da matsananciyar rashin lafiya.
Idriss Deby, wanda ya mutu a watan Afrilun 2022, an maye gurbinsa da dansa, Janar Mahamat Idriss Deby Itno.