Gwamnatin jihar Kaduna tace jami’an tsaro sun kama mutane uku da ake zargin akwai sa hannun da kashe mutane 2 a karamar hukumar Chikun da ke jihar.
Kwamishin tsaro da harkokin cikin Sameul Aruwan shine ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar,cewa an samu cikin wanda yayi sanadiyyar rayukan mutane tare da barnata dukiya a sabon garin dake Chikun a jihar.
A cewar kwamishinan, an saka dokar hana fita ta tsawon sa’o’I 24 domin magance wannan da ta kunno a karamar hukumar.
Aruwan ya bayyana cewa an hana taruwan jama’a Kidan Bashi da gidajen kallo inda nan ake zaton hargitsin ya tashi.
Mutane ukun da ake zargin su da aikata wannan laifin jami’an tsaro sun kama su domin kwantar da tarzoma.
Kwamishinan ya rawaito cewa Gwamna Malam Nasir El-Rufai zai dauki kwakwaran mataki wajen magance tashin hankali a jihar baki daya.