Gwamnatin jihar Kebbi za ta mayar da mutanen da Lakurawa suka raba da garuruwansu

Gwamnan jihar Kebbi, Dakta Nasir Idris ya tabbatar wa mutanen da hare-haren Lakurawa ya raba da muhallansu a jihar cewa gwamnatinsa za ta ɗauki matakan da suke dace domin mayar da su garuruwansu.

Nasir Idris ya bayyana haka ne lokacin da ya kai ziyarar jaje ga mutanen da hare-hare ya raba da garuruwansu a sananin ƴangudun hijira da ke Kangiwa a jihar.

Gwamnan ya kai ziyarar ne domin jajanta wa mutanen tare da ganewa idonsa halin da suke ciki, domin sanin matakin da gwamnatinsa za ta ɗauka, a cewar wata sanarwar da gwamnatin ta fitar.

Al’umomin da suka rasa muhallansu daga garuruwan Birnin Debe da Dan Marke da kuma Tambo, ne ke samun mafaka a sansanin.

A ranar Asabar ne wasu mahara da ake kayuatat zaton na ƙungiyar Lakurawa ne suka ƙaddamar da wasu hare-hare a kauyukan tare da kashe mutum 11 da ƙona ƙauyukan.

Comments (0)
Add Comment