Gwamnatin jihar Kano ta umarci lauyoyinta su yi nazarin umarnin kotun ɗaukaka ƙara

Gwamnatin jihar Kano ta umarci lauyoyinta su yi nazarin umarnin kotun ɗaukaka ƙara na jiya Juma’a, sannan su ɗauki mataki na gaba wanda ya dace da doka.

Gwamnatin ta bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da kakakin gwamna jihar, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar kan bayanin kwamishinan shari’a na jihar, Barista Haruna Dederi a ganawarsa da manema labarai kan umarnin na kotu.

Dederi ya ce hukuncin kotun ɗaukaka ƙara na ranar 10 ga watan Janairu ya tabbatar da soke dokar masarautun Kano na 2019 ne, sannan ya soke hukuncin babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kano.

“Da Alhaji Aminu Babba Ɗan’agundi ya ga bai gamsu da hukuncin ba, sai ya garzaya zuwa kotun ƙoli.”

A cewar kwamishinan, hukuncin kotun ɗaukaka ƙara na farkon na nan daram, “har sai kotun ƙoli ta yanke hukunci wani hukuncin.”

Ya ce wannan umarnin da kotun ɗaukaka ƙara ta bayar, wanda ta buƙaci kowa ya tsaya ya jira hukuncin kotun ƙoli ne, “sanannen abu ne a shari’a.”

Gwamnatin jihar ta yi kira ga jama’a da su kwantar da hankalinsu, sannan su cigaba da gudanar da harkokinsu cikin lumana.

A ƙarshe ya yi godiya ga ƴan jihar a madadin gwamna bisa haƙurinsu da addu’o’in da suke yi domin zaman lafiyar jihar da ma ƙasa baki ɗaya.

Comments (0)
Add Comment