Gwamnatin jihar Jigawa ta amince da ware Naira biliyan 1.1 don siyan karin kayan abinci da suka hada da buhunan shinkafa 12,000 da katan na taliya 15,000 domin sayarwa ma’aikatan gwamnati kan farashi mai rahusa.
Kwamishinan Yada Labarai, Matasa, Wasanni da Al’adu, Sagir Musa ne ya bayyana haka yayin da yake zantawa da manema labarai a jiya kan sakamakon taron majalisar zartarwa ta jiha na ranar Litinin.
Ya ce siyan kayan abincin na daga cikin shirin gwamnatin jihar na samar da shaguna na hadin gwiwa a dukkan kananan hukumomin jihar 27 domin sayar da kayan abinci da sauran muhimman kayayyaki ga ma’aikatan gwamnati kan farashi mai sauki. Sagiru ya bayyana cewa tuni aka samar da hanyoyin kafawa shagunan hadin gwiwa inda ma’aikatan gwamnati za su iya karbar kayan abinci a kan basussuka sannan su biya a hankali.