Gwamnatin Jihar Jigawa zata samar da kamfanin sarrafa takin zamani

Gwamnatin jihar Jigawa zata gina kamfanin sarrafa takin zamani a wani bangare na kokarin habaka ayyukan gona a jiharnan.

Manajin Darakta na kamfanin samar da kayan gona na jihar Jigawa, JASCO, Alhaji Rabi’u Khalid Maigatari, shine ya bayyana haka, yayinda ya kai ziyara zuwa gidan Rediyon Jigawa a Dutse.

Yace samar da kamfanin sarrafa takin zamani zai taimaka wajen cimma kudurin gwamna Muhammad Badaru Abubakar da ma gwamnatin tarayya na wadata kasa da abinci tare da samar da ayyukan yi ga matasa.

Yace gwamnatin jihar Jigawa ta dukufa wajen wadata manoman jihar nan da kayayyakin aikin gona irin na zamani akan farashi mai rangwame bisa la’akkari da kudurin gwamnain tarayya na bunkasa al’amuran aikin gona.

Alhaji Rabi’u Khalid Maigatari yace a yanzu haka kamfanin samar da kayayyakin aikin gona na jiha yayi cikakken tanadi na ingantaccen irin shukawa da magungunan feshi da takin zamani, da taraktoci da injunan girbe shinkafa da na casa da injunan ban ruwa da sauran kayayyaki.

Comments (0)
Add Comment