Gwamnatin jihar Jigawa zata bada taimakon da ya dace domin inganta ayyukan ma’aikatan jihar Zamfara

Gwamnatin jihar Jigawa ta baiwa kwamitin gyara ma’aikata na jihar Zamfara tabbacin bada dukkan goyon baya da taimakon da suka dace domin inganta ayyukan ma’aikatan jihar Zamfara. 

Shugaban ma’aikatan, Muhammad K Dagaceri ne ya bada wannan tabbacin lokacin da ya karbi bakuncin tawagar da suka kawo ziyara jihar Jigawa.

Dagaceri ya yabawa matakin da Zamfara ta dauka na yin nazari a kan sauye-sauyen da Jigawa ta yi. 

Ya kuma ba da shawarar cewa, ya kamata sauran jihohin su yi koyi da jihohin biyu, yana mai jaddada cewa, matakin zai ba da kwarin gwiwa wajen musayar ilimi da samar da ingantacciyar hidima ga jama’a.

A cewar shugaban ma’aikatan gwamnatin, sake fasalin ayyuka a Jigawa ya kunshi kawar da fatara da bunkasa tattalin arziki mai dorewa ta hanyar sabunta ababen more rayuwa da ci gaba. 

Comments (0)
Add Comment