Gwamnatin jihar Jigawa tana daukar nauyin dalibai 210 don yin karatun likitanci a kasar Sudan

Gwamnatin jihar Jigawa tana daukar nauyin dalibai 210 don yin karatun likitanci a kasar Sudan don taimakawa wajen cike gibin da ke akwai a ma’aikatan lafiya.

Mataimakin gwamnan jihar Umar Namadi ya sanar da daukar nauyin daliban a Dutse, yayin ziyarar shugaban kungiyar Editocin Najeriya, Mustapha Isah.

Mataimakin gwamnan ya ce, bayan kammala karatun ana sa ran daliban za su yi aiki a yankunansu daban-daban har zuwa lokacin da aka kayyade.

Ya kara da cewa gwamnatin jihar na shirin tura a kalla likita daya zuwa kowacce cibiya ta kiwon lafiya dake dukkanin yankunan karkara.

Comments (0)
Add Comment