Gwamnatin jihar Jigawa ta nanata kudirinta na bunkasa harkokin ilimi

Gwamnatin jihar Jigawa ta nanata kudirinta na bunkasa harkokin ilmi.

Kwamishinan Ilmi, Dr Lawan Yunusa Danzomo ya bada tabbacin a lokacin bude babban taron shekara shekara na kasa karo na hudu na kungiyar malamai ta kwalejin ilmi da nazarin harkokin sharia ta Ringim ta shirya a makarantar.

Kwamishinan wanda ya samu wakilcin daraktan lura da manyan makarantu na ma’aikatar, Mallam Rabiu Muhammad Dan Gwanki, yace gwamnatin jiha tana tallafawa bangaren ilmi daga matakin farko zuwa na gaba da sikandare domin baiwa matasa ingantaccen Ilmi.

A sakon da ya aike dashi ta hannun Madakin Ringim, Alhaji Bashari Shuaibu, mai martaba sarkin Ringim Dr Sayyadi Mahmud ya yabawa kungiyar malaman kwalejin da mahukuntar kwalejin bisa kokarinsu na bunkasa harkokin ilmi a jihar.

A nasa jawabin mataimakin shugaban kwalejin, Mallam Mutari Sarki ya bayyana alfanun babban taron tare da bayyana gamsuwarsa bisa kyakkywan alakar dake wanzuwa a tsakanin kwalejin da kuma kungiyar.

Comments (0)
Add Comment