Gwamnatin jihar Jigawa ta kashe sama da naira miliyan dubu 5 da miliyan 803 wajen gudanar da ayyukan hukumar samar da ruwan sha a matsakaitan garuruwa daga watan mayun shekara ta 2015 zuwa watan yuni na wannan shekara.
Mukaddashin Manajan Daraktan hukumar, Injiniya Adamu Garba Kiyawa ya sanar da hakan ta cikin wani shirin radio Jigawa.
Adamu Kiyawa ya ce cikin shekaru shida an gudanar da gyaran injinan samar da ruwan sha masu aiki da man gas da masu aiki da hasken rana guda 523 a sassa daban-daban na jihar nan.
Haka zalika an likkafar gidajen ruwa 164 daga masu amfani da man gas zuwa masu aiki da hasken rana.
Manajan Daraktan ya kara da cewa gwamnati ta samar da sabbin na’urorin bada ruwan sha masu amfani da hasken rana guda 514 a mazabun yan majalisar dokokin jiha 30.