Gwamnatin jihar jigawa ta kashe kudi fiye da naira miiliyan 700 wajen gudanar da manyan aiyuka a kwalejin share fagen shiga jami-a ta jiha dake Babura
Shugaban kwalejin Dr Hussain Shehu ya sanar da hakan ta cikin wani shirin Radio Jigawa.
Yace aiyukan da aka gudanar sun hadar da samarwa da kwalejin matsugunni da kewaye kwalejin da gina ofishin gudanar da Mulki da gina dakin kwanan dalibai da aikin hanya mai tsawon kilomita uku da rabi da aikin sanya ruwa da sanya hasken wutar lantarki.
Dr Hussain Shehu ya kara da cewar a bana ma gwamnatin jiha warewa kwalejin kudi naira miliyan 355 a kasafin kudin bana domin gudanar da manyan aiyuka.
Dr Hussain Shehu Yace hukumar bunkasa fasahar sadarwa ta zamani NITDA tana gina katafariyar cibiyar fasahar sadarwa ta zamani wadda suke sa ran mayar da ita zuwa cibiyar rubuta jarabawar shiga jamioi da manyan makarantu ta JAMB.