Gwamnatin jihar Jigawa ta jaddada kudirinta na tallafawa matasan jihar wajen karo Ilimi

Gwamnatin jihar Jigawa ta nanata kudirinta na tallafawa matasa wajen karo Ilimi a mataki daban daban domin amfanin jihar nan da ma kasa baki daya

Kwamishinan Ilmi mai zurfi Dr Isa Yusif Chamo ya bayyana hakan a wajen bikin naurorin komputa ga daliban da suka kammala karatun lawya a bara, a matsayin wani mataki na tallafawa daliban dake karatu aikin lawya

Kwamishinan wanda ya samu wakilcin sakataren zartarwa na hukumar bada tallafin karatu  ta jiha, Malam Saidu Magaji yace gwamnatin jiha ta hannun maaikatar Ilmi ta dade tana daukar nauyin karatun daliban Jigawa anan gida da kuma kasashen wajen domin yin gogayya da sauran daliban kasar nan. Ya kuma taya daliban murnar samun wannan tagomashi tare da fatan zasu yi cikakken amfani da komputa wajen kara samun kwarewar aikin lawya

Comments (0)
Add Comment