Gwamnatin Jihar Borno ta bude sansanin Bakassi ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa

Gwamnatin Jihar Borno, ta bude sansanin ‘yan gudun hijira na Bakassi wanda zai zama mafaka ga wadanda mummunar ambaliyar ruwa ta shafa.

Da tsakar daren ranar Litinin zuwa wayewar Talata, mazauna birnin Maiduguri sun fuaskanci mummunar ambaliyar ruwa.

Lamarin ya faru ne bayan da wani sashe na madatsar ruwan Alu ya fashe da ya haddasa kwarara ruwa zuwa unguwannin da ke kusa.

Cikin wata sanarwa da Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya fitar ta hannun kakakinsa Bayo Onanuga, ya jajanta wa al’umar Borno kan wannan iftila’in.

Shugaban kasar ya bawa gwamnan Jihar Babagana Umara Zulum tabbacin cikakken goyon baya wajen tallafawa wadanda lamarin ya shafa. 

Mataimakin shugaban kasa,Sen. Kashim Shettima, ya kai ziyara Maiduguri don jajanta wa al’uma, inda ya ba da tabbacin cewa gwamnatin tarayya za ta yi duk maiyiwa wajan mayar da mutane gidajensu.

Tuni ya bai wa hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa (NEMA), umarnin kai dauki Maiduguri.

Hukumar NEMA, ta ce tana aiki tare da hukumar bayar da agajin gaggawa ta Jihar Borno (SEMA), wajen samar da taimakon jin-kai ga wadanda ke cikin sansanin.

Comments (0)
Add Comment