Gwamnatin Chadi Tayi Wa Mutum 380 Da Ake Zargi Da Kisan Tsohon Shugaban Kasar Afuwa.

Gwamnatin mulkin soji a Chadi tayi afuwa tare da sakin mutane 380 wanda aka yanke musu hukuncin daurin rai-da-rai bisa zargin su da hannun a kisan tsohon shugaban kaar Idris Deby.
An kashe tsohon shugaban kasar Chadin shekaru biyu da suka wuce, yayinda ya jagoranci yaki da yan tawaye a kasar.
A watan Mayun fiye da yan tawaye 400 aka Yankewa hukunci bisa zargin aikita ta’addanci, da daukar yara aikin soja da kuma cin zarafin shugaban kasar.
Dayawa daga cikin su dan tsohon shugaban kasar Mahamat Idris Deby ya musu afuwa, wanda ya zama shugaban kasar bayan rasuwar mahaifin sa.
Amma kuma afuwar banda jagoran yan tawaye Mahamat Mahdi Ali wanda yanzu haka ya gudu.

Comments (0)
Add Comment