A Najeriya, yayin da matsalar hare-haren ‘yan bindiga ke ci gaba da kamari a yankin arewaci, tsohon ministan tsaro kuma tsohon gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, na ganin rashin yin abin da ya dace wajen fuskantar lamarin ne ya haifar da hakan.
Ya bayyana haka a daya daga cikin shirye-shiryen BBCHausa inda ta rawaito batun.