Gwamnatin Jihar Jigawa ta ware fili mai girman hekta 35 domin gina cibiyar horon harbi ta zamani a Tsohon Kafi da ke Karamar Hukumar Birnin Kudu.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa, SP Lawan Shiisu Adam, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai.
Ya ce wannan shiri na da nufin inganta horon jami’an tsaro da kwarewarsu a fannin harbi, tare da samar da damammakin horaswa ga jami’an soji da sauran hukumomin tsaro. Shiisu ya bayyana cewa wannan ci gaba yana daga cikin kokarin Gwamna Umar Namadi na karfafa tsaro da samar da ingantattun dabarun kariya a jihar. Ya kara da cewa wannan cibiyar horo za ta bayar da damar gudanar da atisayen dabarun yaki cikin tsari da kariya.