Gwamnan Yobe Mai Mala Buni na fuskantar barazanar tsigewa

Masu ruwa da tsakin jam’iyyar APC a jihar Yobe sun bukaci majalisar dokokin jihar da ta tsige gwamna Mai Mala Buni, wanda shi ne shugaban riko na jam’iyyar ta kasa, muddin ya gaza yin murabus.

Sun alakanta bukatar ne da gazawar gwamnan wajen sauke nauyin dake wuyansa, kamar yadda kundin tsarin mulkin kasa ya tanadar a matsayinsa na gwamna.

Masu ruwa da tsakin sun zargin gwamna Buni, da yin shakulatin bangaro da lamurran jihar kacokan, inda yakan ziyarci jihar akalla sau guda cikin tsawon wata 1.

Sun bayyana bukatar ne cikin wata sanarwa da suka fitar bayan wani taro da suka gudanar a Abuja.

Sun ce an zabi Buni ne a matsayin gwamnan jihar ba wai shugaban jam’iyya ba, kuma yasha rantsuwar yin biyayya ga kundin tsarin mulkin kasa, to sai dai a yanzu, yayi watsi da al’umarsa a lokacin da suke bukatarsa.

APCMai Mala BuniPDPYOBE
Comments (0)
Add Comment