Gwamnan Ribas Siminalayi Fubara ya rantsar da shugabannin riƙo na ƙananan hukumomin jihar 23
A yau Laraba ne gwamnan ya rantsar da shugabannin, bayan da da tun da farko majalisar dokokin jihar, ɓangaren da ke biyayya ga gwamnan ya tantance mutanen, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
A ranar Litinin ne wa’adin mulkin tsofaffin shugabannin ƙananan hukumomin waɗanda ke biyayya ga tsohon gwamnan jihar kuma ministan Abuja, Nyesom Wike, ya ƙare. A jiya Talata aka yi rikici a jihar bayan da Gwamna Fubara ya umarci shugabannin sassan mulki na ƙananan hukumomin su karɓi ragamar mulki, amma kuma aka samu hatsaniyar da ta yi sanadiyyar mutuwar mutum huɗu ciki har da ɗansanda ɗay da ɗansakai ɗaya