Gwamnan Kano ya buƙaci gwamnatin Edo ta biya diyyar mafarautan da aka kashe a jihar

Gwamnan Kano ya buƙaci gwamnatin Edo ta biya diyyar mafarautan da aka kashe a jihar

Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya buƙaci Gwamnan jihar Edo, Monday Okpebholo da ya tabbatar da biyan diyyar mafarauta da aka kashe a jiharsa ta Edo a hanyarsu ta komawa gida domin bukuwan Sallah.

Gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin da gwamna Monday Okpebholo ya jagoranci tawagar gwamnatinsa zuwa Kano domin jajantawa gwamnati da al’ummar jihar bisa abin da ya faru na kisan matafiyan a makon jiya.

A jawabinsa, gwamna Abba ya yaba da ƙoƙarin gwamnan na jihar Edo bisa matakan da ya ɗauka, inda ya ce a nasu ɓangaren sun ɗauki matakan da suka dace domin hana ramakon gayya.

Haka kuma, gwamnonin biyu, sun ziyarci garin Torankawa da ke Kano domin jajanta wa al’ummar garin bisa kisan mafarautan nan guda 16 da aka yi a jihar Edo.

Gwamnonin biyu sun ziyarci garin ne da manufar tabbatar wa da iyalan waɗanda al’amarin ya shafa cewa lallai gwamnatin jihar Edo za ta hukunta waɗanda suka yi wannan aika-aika sannan kuma gwamnatin za ta biya su diyya.

A nasa ɓangaren gwamnan jihar ta Edo, Monday Okpebholo ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan inda ya ba su tabbacin cewa gwamnatinsa za ta yi adalci ba daɗewa ba.

Comments (0)
Add Comment