Gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara ya sake rubuta wa majalisar dokokin jihar wasiƙar sanar da ƴanmajalisar aniyarsa ta sake gabatar da kasafin kuɗin jihar na shekarar 2025, domin neman amincewarsu.
Cikin wasiƙar da gwamnan ya aike wa kakakin majalisar dokokin jihar, Martin Amaewhule ranar Alhamis ya ce yana son gabatar da kasafin a gaban ƴanmajalisar a ranar Laraba 19 ga watan Maris, ko a wata rana cikin watan Maris da majalisar ke ganin zai fi dacewa.
Fubara ya ce matakin biyayya ce ga hukuncin Kotun Ƙolin ƙasar, da kuma buƙatar da ƴanmajalisar suka yi masa na sake gabatar musu kasafin kuɗin jihar.
A cikin wasiƙar gwamnan ya tuna wa kakakin majalisar zuwansa zauren majalisar a ranar Laraba da nufin gabatar da kasafin, amma sai aka kulle ƙofar aka hana shi shiga tare da tawagarsa.
“Za ka iya tuna ziyarar da kawo majalisar a ranar Laraba 12 ga watan Maris domin gabatar da kasafin, domin biyayya ga hukuncin Kotun Ƙoli, amma ba a ba ni damar shiga zauren majalisar ba”, kamar yadda wani ɓangare na wasiƙar ya nuna.