Gwamnan jihar Neja ya bayyana rashin gamsuwarsa kan yadda NAHCON ta gudanar da shirye-shiryen aikin Hajji bana

Gwamnan jihar Neja Mohammed Umar Bago ya bayyana rashin gamsuwarsa kan yadda hukumar alhazan Najeriya Nahcon ta gudanar da shirye-shiryen aikin Hajji bana.

Yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai a Saudiyya game da yadda aka gudanar da aikin, Gwamna Bago ya yi kira ga majalisar dokokin ƙasar ta binciki Nahcon kan yadda ta kashe kuɗin tallafin aikin hajji na naira biliyan 90 da gwamnatin tarayya ta bai wa hukumar.

Gwamna Bago ya ce a matsayinsa na gwamna zai buƙaci ƙungiyar gwamnonin ƙasar ta yi kiran rusa hukumar Nahcon, saboda a cewarsa hukumar ba ta da wani amfani, ta gaza ta kowane fanni.

Ya ce ya kamata shirya aikin Hajji ya koma ƙarƙashin ikon jihohi ba gwamnatin tarayya ba.

Gwamnan ya kuma nuna damuwarsa kan yadda ya ce Nahcon ta kasa samar wa gwamnoni da sauran manyan mutane masaukai a Minna.

Comments (0)
Add Comment