Gwamnan jihar Kogi ya nemi gwamnatin tarayya da ta taimakawa jihar wajen yaki da matsalar tsaro da ambaliyar ruwa

Gwamnan jihar Kogi Ahmed Usman Ododo ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta taimakawa jihar wajen yaki da matsalar tsaro da kuma ambaliyar ruwa a wasu sassan jihar.

Mataimaki na musamman ga gwamnan akan sha’anin yada labarai , Ismaila Isah a cikin wata sanarwa da ya fitar, ya Ambato gwamna Ododo na yin kiran ne a lokacinda ya karbi bakuncin wata kungiya mai tattara haraji da kula da fasalin kasa a gidan gwamnatin jihar.

Gwamnan ya bayyana cewa a matsayin na jihar da tayi iyaka da babban Birnin tarayya Abuja, da kuma wasu jihohi goma, jihar ta kogi tana bukatar karin kudade daga gwamnatin tarayya domin magance kalubalen tsaro da kuma na ambaliyar ruwa. Ododo yace matsalar tsaro da ambaliyar ruwa da jihar ke fama dashi zasu iya shafa babban Birnin tarayya da kuma wasu jihohi makota in har ba’a dakile lamarin ba.

Comments (0)
Add Comment