Gwamnan jihar Kano ya nemi karin kasafin kudi domin biyan sabon mafi karancin albashi

Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya rubutawa majalisar dokokin jihar bukatar amincewa da karin kasafin kudin shekarar 2024 da N99.2B domin biyan sabon mafi karancin albashi.

Sai dai an karanta wasikar bukatar gwamnan a zauren majalisar yayin zaman da kakakin majalisar, Ismail Falgore ya jagoranta.

A Falgore, gwamnan yana neman amincewarsu ne bisa sashe na 122 (A da B) na kundin tsarin mulkin kasar na 1999 domin kara kaimi da aiwatar da ayyukan da suka sa a gaba da nufin inganta rayuwar ‘yan jihar.

Yayin da yake nanata kudurin gwamnati na mai da hankali kan raya ababen more rayuwa, bunkasa jarin yan jihar, inganta fannin kiwon lafiya da ilimi, Shanono ya jaddada cewa karin kasafin kudin zai kuma kunshi sabon mafi karancin albashi da sauran su.

Sai dai dan majalisar da ke wakiltar mazabar Nasarawa a majalisar dokokin jihar Kano, Yusuf Aliyu, ya gabatar da kudirin yin kira ga gwamnatin jihar da ta gyara tare da sake gina filin wasa na Gwagwarwa domin yakar ta’addancin safarar miyagun kwayoyi da rashin tsaro a tsakanin al’umma.

Comments (0)
Add Comment