Gwamnan jihar jigawa yayi kira ga manoma da makiyaya su rungumin zaman lafiya a tsakanin su

A wani yunkuri na tabbatar da zaman lafiya da walwala gwamnan jihar jigawa Umar Namadi yayi kira ga manoma da makiyaya su rungumin zaman lafiya a tsakanin juna.

Da yake jawabi yayin wata ziyarar sasanto a kauyen Kabak dake karamar hakumar Kirikasamma, gwamna Namadi ya jaddada muhimmancin zaman lafiya domin bunkasar cigaba da karuwar tattalin arziki a yankin.

Yayi gargadi kan kutsen makiyaya da cin iyaka ba bisa ka’ida ba yana mai cewa gwamnati zata dauki tsauraran matakai na ladabtar da masu aikata laifi.

Shugaban kungiyar manoma na kasa reshen jihar Jigawa Maiunguwa Jaga, ya yabawa gwamna bisa daukar matakain gaggawa domin sasanta rakicin manoma da makiyaya daya dade yana addabar al’ummar jiha.

Sawaba radio ta bayar da rahotan yadda rikicin manoma da makiyay ya kwashe shekaru da dama yana sanadin salwantar da rayuka da dukiyoyi.

Comments (0)
Add Comment