Gwamnan jihar Jigawa ya bukaci ‘yan jarida da su kasance masu gaskiya da adalci a cikin rahotonnin su

Gwamnan jihar Jigawa Mallam Umar Namadi ya bukaci ‘yan jarida dake bakin aiki da su kasance masu gaskiya da adalci a cikin rahotonninsu.

Gwamnan ya yi wannan kiran ne a lokacin da ya karbi bakuncin ’yan kungiyar wakilan kafafen yada labarai reshen jihar Jigawa, wadanda suka kai masa ziyarar ban girma a gidan gwamnati da ke Dutse, babban birnin jihar.

Mallam Umar Namadi, ya yi kira ga ‘yan jarida dake bakin aiki da su goyi bayan kudirin gwamnatinsa na kawo cigaba a jihar da kuma cimma manufofin da aka sanya a gaba. Shugaban kungiyar wakilan kafafen yada labarai reshen jihar Jigawa, Kwamared Muhammad Zangina Kura, ya ce mambobin kungiyar sun je gidan gwamnati domin taya gwamnan murnar samun nasarar karbar rantsuwa da kama aiki.

Comments (0)
Add Comment