Gwamnan jihar Jigawa Malam Umar Namadi ya nemi goyon baya da hadin kan ma’aikatan jihar domin ciyar da jihar gaba.
Ya bayyana hakan ne a jiya a yayin wani taro da daraktoci da mataimakansu da aka gudanar a dakin taro na Sir Amadu Bello da ke sabuwar sakatariyar jiha a Dutse babban birnin jihar.
Malam Umar Namadi ya kuma bukaci daraktocin da su rika horas da wadanda ke karkashinsu domin maye gurbinsu yadda ya kamata, idan sun yi ritaya daga aiki.
Gwamnan ya ce makasudin taron shi ne tattauna batutuwan da suka shafi yadda za a inganta ayyukan gwamnati da jin dadin ma’aikata.
A jawabinsa na maraba shugaban ma’aikata na jiha Alhaji Hussaini Ali Kila ya bada tabbacin cewa ma’aikatan za su bada gudunmawar domin cigaban jihar.