Gwamna Zulum Ya Kaddamar Da Ginin Gadar Sama Mai Tsawon Mita 600 A Maiduguri

Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno ya kaddamar da aikin gina gadar sama mai tsawon mita 600 a tashar Borno Express dake birnin Maiduguri a jiya asabat.
Aikin wanda shi ne irinsa na biyu a Maiduguri zai lakume naira biliyan 5.8.
Gwamnan ya ce gadar za ta kara rage cunkoson ababen hawa a yankin tare da kara samar da ababen more rayuwa a babban birnin jihar.
Ya kara da cewa gwamnati za ta tabbatar da fitar da kudaden aikin cikin gaggawa.
Gwamnan ya ba da kwangilar gina gadar ga wani kamfanin kasar China wanda ake sa ran kammala aikin kafin karshen shekarar 2023.

Comments (0)
Add Comment