Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya yi alkawarin ceto dukkan daliban da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a garin Kuriga da ke karamar hukumar Chikun a jiya Alhamis.
A ziyarar da Gwamnan ya kai wa al’ummar yankin domin jajanta musu a kan lamarin, Gwamnan ya tabbatar wa al’ummar yankin goyon bayan Shugaba Bola Tinubu da kuma mai ba Shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu akan lamarin.
Duk da cewa har yanzu ba a tabbatar da adadin yaran da aka sace ba, Gwamnan Sani ya bukaci al’umma da su kwantar da hankalinsu tare da hada kai da gwamnati wajen ganin an sako yaran.
Ya kuma bayyana cewa za a kafa kwamitin tsaro a Kuriga tare da neman a kafa sansanin soji a yankin domin karfafa tsaro.