Gwamna Mallam Umar Namadi ya bada umarnin daukar matakan gaggawa domin dakile bullar ambaliyar ruwa a daminar bana.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da babbar mataimakiya ta musamman ga gwamnan jiha Kan Kafafan Yada Labarai , Hajia Zainab Shuiabu Rabo Ringim.
Tace Gwamna Mallam Umar Namadi ya bada umarnin ne a lokacin taron tattaunawa da mahukuntan maaikatar kare mahalli ta jiha.
Ya ce daukar matakan ya zama wajibi domin ganin an kare rayuka da kuma dukiyoyin alummar jihar nan
Mallam Umar Namadi ya bada umarnin yin aikin jinga a dukkannin wuraren da ake da kokontan samun ambaliyar ruwa a bana , yayinda ya sake bada umarnin kaiwa kayayyakin aikin jinga zuwa wadannan wuraren domin yin aikin jinga tare da alummomin da abin ya shafa
Gwamnan ya bada umarnin kafa kwamiti mai wakilai tara domin zagaya wuraren da za a yi aikin jingar , inda kuma ya nemi hadin kai da goyan bayan alumomin da abin yashafa