Gwamna Namadi ya ƙarɓi kundin rahoton sakamakon tantance ma’aikatan jihar Jigawa

Gwamnan jihar Jigawa Mallam Umar A. Namadi ya ƙarɓi kundin rahoton sakamakon tantance ma’aikata da aka yi  a shekarar da ta gabata, wadda aka yi shi domin haɗe bayanan ma’aikata a cikin manhajar  biyan albashin bai daya na IPPS ga dukkan ma’aikatan jihar Jigawa.

Idan dai za’a iya tinawa sawaba radio a baya ta waito cewa gwamna Mallam Umar Namadi ya bayar da umarnin gaggauta tantance ma’aikatan tare da sanya su cikin tsarin biyan albashi na manhajar IPPS.

Wasu daga ma’aikata a kananan hakumomi sun kwarmaton kin amincewa da salon yadda aikin ke tafiya a fadin jiha.

Sakataren gwamnatin jihar Jigawa Alhaji Bala Ibrahim Mamsa a tattaunawar sa da wakilin sawaba yayin bikin Sallar gani a masarautar Hadejia, ya bayyana dalilin shirin tantance ma’aikatan jihar Jigawa.

Comments (0)
Add Comment