Gwamna Muhammad Badaru Abubakar ya amince da nadin Sa’idu Magaji a matsayin babban sakatare a ma’aikatar tallafin karatu ta jiha.
Wannan dai na kunshe cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun sakataren gwamnatin jiha Alhaji Adamu Abdulkadir Fanini
Kafin nadin nasa ya kasance mukadaddashin sakataren ma’aikatar.
Sanarwar ta kuma kara da cewa nadin ya fara aiki nan take.