Gwamna Muhammed Badaru Abubakar na nan Jihar Jigawa ya bayyana tsohon shugaban hukumar Shige da Fice ta Kasa Muhammed Babandede a matsayin Jakada Nagari ga Jihar nan.
A cewarsa, duk yan kishin Jihar nan Maza da Mata, zasu yi Alfahari da yadda ya hidintawa kasar nan, tare da kare mata mutumcinta ta fannin hukumar sa.
Gwamna Badaru ya bayyana hakan ne a lokacin da tsohon Kwamfuloran ya kai masa ziyara a gidansa dake Kano, domin gode masa kan gudunmawar da ya bashi tsawon shekaru 5.
Gwamnan Badaru ya ce duk dan Jihar nan yana Alfahari da Babandede bisa yadda ya zama wakili Nagari ga Jihar Jigawa a matakin kasa.
Gwamnan, ya taya Babandede murnar kammala aikinsa Lafiya, da kuma irin Nasarorin da ya samu a lokacin aikin nasa.
Tun farko a Jawabinsa, Alhaji Muhammad Babandede, ya godewa Gwamna Badaru kan goyan baya da karfafa gwiwar da ya bashi a lokacin da yake Jagorantar hukumar.