Gwamnan jihar Jigawa Muhammadu Badaru Abubakar ya amince da tura Alhaji Bala Ibrahim Mamsa a matsayin sabon kwamishina a ma’aikatar yada labarai, matasa, wassani da al’adu ta jiha.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa dauke da sa hannun sakataren gwamnatin jiha, Alhaji Adamu Abdulkadir Fanini, wacce aka rabawa manema labarai a Dutse.
- Majalisar Dokokin Legas ta sake zaɓen Obasa a matsayin kakakinta
- An yi garkuwa da wani ɗansanda a Abuja
- Gwamnatin Jihar Yobe ta bayar da tallafin karatu da ya kai Naira biliyan 2.22 ga dalibai 890
- Kungiyar NANS ta yi barazanar fara zanga-zanga a fadin Najeriya
- Kotun ta yi watsi da bukatar hana jami’an gwamnati tafiya kasashen waje don neman magani
Sanarwar tace gwamnan ya kuma amince da canja Alhaji Muhammad Alhassan daga ma’aikatar yada labarai, matasa, wassani da al’adu zuwa ma’aikatar aikin gona da ma’adanan kasa, a matsayin kwamishina.
Sanarwar ta yi kira ga kwamishinonin da su sadaukar da kawunansu wajen tabbatar da samun nasarar kudirori da tsare-tsaren gwamnatin Badaru, domin cigaban jihar baki daya.