Gwamna Muhammad Badaru Abubakar na nan Jihar Jigawa ya ce gwamnatin sa zata kara fadada Makiyayar Fulani a sassan Jihar nan.
Wannan na kunshe cikin wata sanarwa da Kakakin sa Alhaji Habibu Nuhu Kila, ya rabawa manema labarai a Dutse.
Alhaji Habibu Nuhu Kila, ya ce gwamna Badaru Abubakar, ya bada tabbacin hakan ne a lokacin da yake ganawa da Shugaban Kungiyar Miyatti Allah Kautal Hore Alhaji Umar Kabir a gidan gwamnati.
Gwamna Badaru, ya bukaci kungiyar ta tallafawa kudurin gwamnatinsa na dakile laifuka a tsakanin Fulani, musamman Matasan da suke aikata laifuka.
Kakakin Gwamnan ya rawaito wurin da Gwamna Badaru ya ke daukan alkawarin samar da ilimi ga yan jihar nan, ciki harda Fulani.
A jawabinsa, Shugaban Kungiyar ya yabawa gwamnatin jiha bisa samar da zaman lafiya a jihar nan.
Haka kuma, ya ce Kungiyar zata bawa gwamnati dukkan goyan bayan da take bukata domin samar da zaman lafiya a tsakanin Fulani da Makiyaya a jihar nan.