Gwamantin Tarayya ta ce ba ta da masaniya game da batun sayo makamai na Dala miliyan 875 daga Amurka

Gwamantin Tarayya ta ce ba ta da masaniya game da batun sayo makamai na Dala miliyan 875 daga Amurka da Majalisar Dokokin Amurka ta hana a sayar wa Najeriya.

Ministan yada labarai da Al’adu Alhaji Lai Muhammad, ya bayyana labarin da ake yadawa a matsayin na bogi.

A yayin da yake jawabi ga kamfanin dillancin labarai na kasa NAN a yau juma’a a Abuja, ministan ya ce, babu wata yarjejeniyar sayen makamai tsakanin Najeriya da Amurka in banda ta sayen jirage masu saukar ungulu kirar Super Tucano 12 wadanda shida daga cikin sun riga da sun iso, za kuma a kaddamar dasu a ranar 3 ga watan Agustan gobe.

A cewar ministan, dangantaka tsakanin Najeriya da Amuraka na tafiya dai-dai yanda ya kamata.

Comments (0)
Add Comment