Guguwa mai tafe da mamakon ruwan sama ta hallaka mutane a yankin gabashin Libya

Aƙalla mutum dubu biyu ne suka rasu da dama kuma suka ɓace bayan da wata mahaukaciyar guguwa mai tafe da mamakon ruwan sama ta haddasa ambaliya a yankin gabashin Libya.

Ruwan ya janyo mummunar ambaliya tare da zaftarewar ƙasa da kuma lalata gidaje da tituna da dama a yankin.

Zuwa yanzu dai rahotanni na nuna cewa wajen da wannan ambaliya ta fi yuwa barna shi ne birnin Derna mai tashar jirgin ruwa inda madatsun ruwa biyu da kuma gadoji hudu suka rushe.

Kuma galibin birnin na cikin ruwa tsundum.

An ayyana yankin a matsayin wanda mummunan iftila’I ya afka wa tare da ayyana kwana uku na makoki.

Bayanai sun nuna cewa abu ne mai wuya a iya bayyana yawan mutanen da suka halaka saboda babu hanyoyin sadarwa sosai.

Sannan kuma ga rashin tartibiyar gwamnati, sakamakon yaƙin da aka kwashe wajen shekara goma ana yi tsakanin manyan abokan gaba biyu a ƙasar.

Sojojin ƙasar ta Libya bakwai ne aka bayar da rahoton sun ɓace a lokacin da suke aikin agaji.

Tun a ranar Lahadi ne mahaukaciyar guguwar mai tafe da ruwa da aka yi wa lakabi da Daniel ta sauka a ƙasar ta Libya.

Comments (0)
Add Comment