Gobara ta ƙone wasu sassa na shahararriyar Kasuwar Gomboru da ke Maiduguri

Wata gobara ta ƙone wasu sassa na shahararriyar Kasuwar Gomboru da ke Maiduguri, babban birnin Jihar Borno.

Bayanai sun ce gobarar dai ta tashi ne a ɓangaren ’yan Katako da ke cikin kasuwar inda ake sayar da itace da kayan kafinta.

Wani ganau da ke wurin ya ce zuwa yanzu ba za a iya tantance barnar da gobarar ta yi ba amma an shawo kan lamarin.

Ya ce gobarar ta tashi ne da misalin karfe 9:50 na dare, inda shaguna da dama suka ƙone a lokacin da jami’an kashe gobara suka isa cikin ta ‘yan mintuna. A bara ma Kasuwar Gomboru dai ta sami irin wannan bala’i na tashin gobara.

Comments (0)
Add Comment