Shugaban kwamitin majalisar wakilai mai kula da ilimin jami’o’i, Dr. Abubakar Hassan Fulata ya gabatar da bukatar biyan malaman firamare albashi dubu dari biyu da hamsin a kasar nan.
Ya kuma shigar da bukatar Naira miliyan daya a matsayin albashin malaman jami’oi.
Dan majalisar ya ce matakin zai inganta harkar koyo da koyarwa a najeriya
Ya ce gwamnatin tarayya ta cire Jami’o’i daga tsarin biyan lbashi na bai daya wato IPPIS.
A cewarsa gwamnatin tarayya za ta ware kudi a cikin kasafin kudin shekarar 2025 domin kaddamar da sabuwar kwalejin noma ta tarayyaa Kiri-Kasamma da Kwalejin Ilimi ta tarayya a Birniwa.