Shugaban jamhuriyar Demokradiyyar Kongo Félix Tshisekedi yayi kira ga dakarun majalisar dinkin duniya su fice daga kasar a wannan shakara.
Ya fadawa babban taron majalisar dinkin duniya jiya, cewa, ya umarci gwamnatin sa ta fara tattaunawa da shugabannin dakarun su kwashe kayan su daga decembar shekarar nan zuwa karshen 2024.
Tshisekedi yace shirin wanzar da zaman lafiya a kasar ya kasa cimma nasara tsawon shekaru 25.
Tawagar malisar dinkin duniya mai aiki kwantar da tarzoma a kasar ta kunshi dakaru dubu 18, ciki har da sojoji sama da dubu 12, abin da ya sanya ta zama tawaga mafi girma ta 2 a duniya.
Sai dai ta gamu tsegumi a shekarun baya-bayan nan bayan zanga-zangar nuna kin jini tun a bara. Masu zanga-zangar sun soki dakarun da kasa tsare fararen hula na sama da shekaru 10, yayin da yan aware ke kaddamar da ayyukan su a kasar mai arzikin man fetur.