EndSARS: Burtaniya ta yabawa Nigeriya saboda saurar ra’ayyin yan kasa

Kasar Burtaniya ta jinjinawa gwamnatin tarayya bisa amsa kiran yan kasa na soke rundunar yan sanda dake yaki da ayyukan fashi da makami wato SARS.

Babbar kwamishiniyar Kasar a Najeriya Catriona Laing, ta bayyana matakin a matsayin abin a yaba.

Ta bayyana hakane a shafinta na Twitter inda ta wallafa cewa, sanarwar gwamnatin tarayya dangane da makomar SARS abin a yaba ne.

Ta bayyana jajircewar shugaban yansanda Mohammad Adamu wajen kawo karshen cin zarafin yan adam da rundunar keyi da ma tabbatar da an kiyaye martabarsu, a matsayin abinda zai dawowa da al’umma kwarin gwiwa kan hukumar tasu.

Ta bukaci hukumomi da kiyaye yancin al’uma na gudanar da zanga zanga, tana mai kira ga masu zanga zangar, da gudanar wa cikin lumana.

Nigeria
Comments (0)
Add Comment